‘Yan Majalisa na neman alfarma daga ma’aikatu ganin zabe ya kusa
- Shugabannin Hukumomi sun fallasa ‘Yan Majalisar Tarayya
- ‘Yan Majalisa na neman alfarma daga wasu ma’aikatun Kasar
- Majalisar na kawowa wanda bai biya masu bukata ba cikas bana
Shugabannin Hukumomin Tarayya na kasar nan sun bayyana cewa su na samun matsin lamba daga ‘Yan Majalisar Taraya domin su ba mutanen su aiki kafin su amince da kasafin kudin su ganin 2019 ta karaso kaso gaf-da-gaf.
Wani Bawan Allah wanda yake shugabancin wata Ma’aikatar Tarayya ya bayyanawa Jaridar Sahara Reporters cewa ‘Yan Majalisar Tarayya na kokarin tursasa su domin su ba jama’a aiki kafin a amince da kundin kasafin kudin su.
KU KARANTA: TY Danjuma ya nemi jama'a su kare kan su a Najeriya
A dalilin hakan ne dai wasu da dama su ka gaza bayyana a gaban Sanatoci da ‘Yan Majalisa domin su gabatar da kasafin kudin su. Kwanakin baya dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi su yi maza a kare kasafin kudin su.
Da zarar an ki ba Sanatocin abin da su ke nema dai sai su nemi su kawowa mutum cikas a Majalisar. Wani Sanata a Kasar Sonny Ogbuoji ya musanya wannan zargi inda ya bayyana cewa karya kurum ake yi wa abokan aikin sa ‘Yan Majalisar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng