Fina-Finan mu tamkar madubin rayuwar Hausawa su ke - Alhassan Kwalli
A yayin ganawa da manema labarai na mujallar karshen mako ta kamfanin jaridar Daily Trust, fitaccen jarumi kuma shugaban cibiyar jaruman hausa, Alhassan Kwalli, ya yi karin haske dangane sa wasu al'amura da suka shafi sana'ar su ta shirya fina-finai.
Jarumin dai ya bayyana cewa, babbar manufa ta wannan cibiya a matsayin sa na jagoranta shine tabbatar da hadin kai a tsakanin dukkan jarumai tare da kare hakkokin su a fagen sana'ar su.
Alhassan Kwalli ya ci gaba da cewa, ya yi matukar murna da wannan ganawa ta sa da 'yan jarida inda ya hikaito ma su irin ci gaba da su ke samu a fagen sana'ar su da a yanzu sun zamto tamkar madubin dubawa na rayuwar al'umma.
Fitaccen jarumin yake cewa, ba bu shakka fina-finan su sukan haskaka al'adun hausawa wanda a yanzu sun zamto kwatankwacin rayuwar su.
A yayin tuntubar sa dangane da yadda gwamnati ke mu'amalantar su, Jarumi Alhassan Kwalli ya bayyana cewa, ko shakka ba bu akwai kyakyawar fahimta da kuma alaka mai karfin gaske tsakanin su da gwamnati.
KARANTA KUMA: Zazzaɓin Lassa ya shiga birnin tarayya, ya fara tabargaza
Jarumin ya ce a wani sa'ilin gwamnati ta kan nemi shawararin su da gudunmuwa wajen wayar da kawunan al'ummar ta.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar 'yan sanda ta hana jam'iyyar PDP aiwatar da wani gagarumin taro da ta shirya gudanar wa a jihar Kano.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng