Ceto 'yan matan Dapchi da makomar Arewacin Najeriya, rubutun Abdurrazak Ibrahim

Ceto 'yan matan Dapchi da makomar Arewacin Najeriya, rubutun Abdurrazak Ibrahim

- An ceto matann Dapchi ne bayan da aka tattauna da mayakan Boko Haram

- Hotuna sun nuna samari na yaba wa 'yan ta'addanr

- Marubucin na ganin Arewa ta shiga uku

Ceto 'yan matan Dapchi da makomar Arewacin Najeriya, rubutun Abdurrazak Ibrahim
Ceto 'yan matan Dapchi da makomar Arewacin Najeriya, rubutun Abdurrazak Ibrahim

Abdulrazak Ibrahim: 'Dawowar ‘Yan Matan Dapchi da kuma alkiblar Arewacin Najeriya'

Dawowar yawancin ‘yan matan Dapchi labara ne mai dadi. Amma cigaba da rikon jarumar yarinyar nan Leah Sharibu, wadda taki tursasar shiga musulunci a hannun ‘yan ta’adda, abun damuwa ne kuma dabara ce ta yin ta’addanci

Murnar da taron samari suka yi a garin Dapchi yana nuna abunda yawancin mutane ke tsoro; Idan har da Boko Haram zasu ci nasara a yankin, sai ma kaga cikin shekaru masu zuwa, ana bayyanasu a matsayi masu neman ‘yancin kai.

Dawowar yawancin ‘yan matan Dapchi labara ne mai dadi. Hakan yana nuna dabarar ‘yan kungiyar ta Boko Haram bangaren ISIS son su nuna cewa sunfi ‘yan bangaren Shekau alamun son zaman lafiya.

Kila hakan nan gaba zai sa su sami karin mayaka a yankin, wanda shine abin da ya kamata ya razana duk mai hankali. Gaskiyar magana itace muna cikin gagarumar matsala, saboda burin ‘yan kungiyar ta Boko Haram shine ta mayar da Najeriya kasar musulunci, hanyar dazasu cimma burinsu itace su ringa yin irin wadannan abubuwan na nuna tausayi duk da a zahiri basu da shi.

DUBA WANNAN: Garin soyayya ta mutu a Otal, ya binne ta a daji ya gudu

Baza’a iya samun nasara akan Boko Haram ba ta hanyar yin yarjejeniya da musayar mutanen da suka kama, ko don kudin fansa, ko ma musayar mutanensu da aka kama, su abin da suka sanya gaba shine so su mayar da Najeriya kasar musulunci. Hanyar da za’ayi nasara akan wannan matsala itace ta nunawa jama’a kin yarda da manufofinsu a akidance da ilimi.

Dole mu raba addini da siyasa, saboda hakan yana koyar da yaranmu cewa ba wani abun damuwa bane ka nuna kiyayya ga wani don ba addininku daya ba. Kamar yadda muke yi a yanzu.

Sai mun koma mun fara tattaunawa da junanmu kan yadda ya kamata mu mu'amalanci junanmu da makwabtanmu, sannan ne zamu iya gane wa al'ummar mu maita mai dore wa, cike da ilimi, son juna da rashin zafin kishi na ba gaira babu dalili.

Dakta Abdurrazak Malamin ilimin Kimiyya ne a Jami'ar Ahmadu Bello.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: