Garin soyayya da mai aure a Otal aka mutu, ko garin yaya, biyo labarin

Garin soyayya da mai aure a Otal aka mutu, ko garin yaya, biyo labarin

- Su dai ma'aurata akan sa rai su kadai ke iya hucewa juna sha'awa da shauki

- Lamarinn ba haka yake ba a tsakanin jama'ar zamanin nan

- An rasu a Otal ana tsaka da masha'a

Garin soyayya da mai aure a Otal aka mutu, ko garin yaya, biyo labarin
Garin soyayya da mai aure a Otal aka mutu, ko garin yaya, biyo labarin

Musliu Owolabi dai makanike ne dan shekaru 36, wanda ya dauki budurwarsa bazawara Fausat Idowu, Otal domin kada kuri'arsa ta soyayya a jihar Ogun, bayan da cewa kuma yana da nasa iyalin a gida, sai dai kuma matar ta cika a hannunsa a Otal din.

Tsoron kar iyali da jama'ar gari su gane sai mutuminka ya kwashi gawar ya kai daji ya binne, ya koma gida abinsa yaci gaba da rayuwarsa.

Yanzu dai hukumar 'yansanda ta kamo shi ta rutsa shi da tambayoyi, inda kuma ta sami bayanai na inda ya kai gawar ya bizne.

DUBA WANNAN: Auren mata hudu ko shida a tare, sabon yayi da baya daga wa mata hankali

An gano wayar tane da kuma yadda shi tayi wa wayar karshe, daga nan ta tsallake yayanta hudu ta ce ta tafi bikin suna, tun 1 ga Fabrairu.

Shi dai gogan yace suna tsaka da soyayya ne abubuwa suka rikice, inda da yaga abu yayi kamari, ya garzaya da ita asibiti, ammma ta cika a hanya, shi kuwa kawai ya tafi ya binne ta ya koma gida.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: