Manzo Jarmaya Fufeyun ya sayi jirgin sama, yace a taya shi murna

Manzo Jarmaya Fufeyun ya sayi jirgin sama, yace a taya shi murna

- Pastoci dai basu fiye wani aiki ko sana'a ta neman kudi ba

- Aikinsu tilo shine wa'azi mai ratsa jiki

- Su kuma mabiya akwai sadaka muddin coci ta nema

Manzo Jarmaya Fufeyun ya sayi jirgin sama, yace a taya shi murna
Manzo Jarmaya Fufeyun ya sayi jirgin sama, yace a taya shi murna

Pastor dai sukan kira kansu annabawa da ke karbar wahayi daga ubangiji, inda sukan ce, an gaya musu cewa mabiya zasu tara musu kudi domin su sami wani abinn alfarma ko alatu, ko ma warware wa kansu matsalolin rayuwa.

Hakan ya sanya coci ta zama watacibiya ta tara uban kudi da babu hisabi kansu, domin ko gwamnati bata bibiyar wadannan kudaden zakka da sadaka domin haraji.

Su daii wadannan kudade ana kiransu Tithe, kuma sun arzurta da yawa daga cikin manyan Pastoci da annabawan zamani.

DUBA WANNAN: An kama kawalai dake sanya mata a karuwanci

Ba abin mamaki bane a zamanin nan kaga Pastor a jirginsa na kansa, ko mota, ko ababen more rayuwa a cocin da take da yawan talakawa.

Su talakawan masu bada sadaka duk rana ko sati, sukan biya kaso daya bisa goma ne na duk abin da suka samu na arziki, inda akan basu tsoro da cewa zasu mutu, ko gidansu zai gobara ko zasu haukace in basu biya ba.

Idan coci tana neman taimako, sai tace talakka su hado kudi, in su kuma suka ce suna neman kudi, sai ace suyi addua Allah zai basu.

Haka ma tsaro, sai kaga masu kiran kansu annabawa sun dauki hayar masu kare lafiyarsu da ta iyalansu da jibga-jibgan bindigogi, amma su talakawan sai ace musu suyi addua, ai wai mala'iku ke kare su.

Prophet Jeremiah Omoto Fufeyin dai shima yabi sahun takwarorinsa a gasar sayen motoci da jiragen sama, inda yace jama'a su taya shi murna, Allansa ya yassare masa ya sayo jirgi, domin yawon wa'azi a duniya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel