Shugaba Buhari ya aika da sakon gaisuwa akan rashin Surukin tsohon shugaban kasa Obasanjo
A ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya aika da sakon sa na gaisuwa zuwa ga iyalan Abebe, gwamnati da kuma al'ummar jihar Edo a sakamakon rashin Dakta Christopher Abebe da ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayi Abebe dai ya kasance mahaifi ga Stella, marigayiya matar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Shugaba Buhari a sanarwa sa ta ranar Juma'a da sanadin mai magana da yawun sa Mista Femi Adesina, ya jajintawa iyalan surukin Obasanjo, 'yan uwa da abokan arziki tare da gwamnati da kuma al'ummar jihar Edo a sakamakon wannan babban rashi da su ka yi.
Tarihi ya bayyana cewa, Marigayi Abebe ya kasance shugaban kamfanin United Africa Company, shugaban jami'o'in Benin, Nsukka da kuma Calabar a yayin rayuwar sa.
KARANTA KUMA: Wani Mahaifi ya salwantar da rayuwar dan sa kan Kwallon Kashu a jihar Enugu
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Marigayi Abebe yayin rayuwar sa ya kasance mutum mai matukar kishin kasar sa da kuma jajircewa akan harkokin sa na kasuwanci.
Shugaban kasa Buhari ya kuma yi addu'a ta neman samun nutsuwa da kwanciyar hankali a makwancin Abebe tare da bayar da hakuri ga duk wadanda su ke baƙin cikin rashin surukin na tsohon shugaba Obasanjo.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, zazzabin Lassa ya tsallaka birnin tarayya ya fara cin karen sa ba bu babbaka.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng