Guguwar kankara ta jefa mutane milyan 70 cikin tashin hankali
- Sama da Amurkawa milyan 70 ne suke cikin halin kaka - ni - kayi, sanadiyyar wata guguwar kankara data addabesu
- Guguwar wacce ta sako kai da tsakiyar daren Laraba a yankin Philadelphia da kuma yankin Washington D.C, inda a jiya Alhamis guguwar ta isa birnin New York
Sama da Amurkawa milyan 70 ne suke cikin halin kaka - ni - kayi, sanadiyyar wata guguwar kankara data addabesu.
DUBA WANNAN: Arewa ita ce babbar matsalar Najeriya - Inji Dattawan Yarabawa
Guguwar wacce ta sako kai da tsakiyar daren Laraba a yankin Philadelphia da kuma yankin Washington D.C, inda a jiya Alhamis guguwar ta isa birnin New York.
Dalilin da yasa aka rufe dukkanin makarantu, ma'aikatun gwamnati da masana'antu dake cikin birnin Washington D.C a wuraren da guguwar ta shafa.
A birnin New York kuma annobar tayi sanadiyyar dakatar da zirga - zirga a kan hanyoyin jirgin kasa, inda a New Jersey kuma hanyoyin sufuri na motoci ne suka samu matsala gabaki daya.
Manyan masana a fannin hasashe na yanayi sun bayyana cewa guguwar kankarar zata cigaba da yaduwa har zuwa yankunnan Amurka, wanda suka hada da Massachusetts, Connecticut da kuma Maine, sannan daga baya masanan sun bayyana cewar akwai yiwuwar guguwar ta haifar da ambaliyar ruwa a yankin gabar tekun Atlantik.
Daga ranar Talatar wannan satin zuwa jiya Alhamis, kamfanin jirgin sama na Amurka mai suna Flight Aware ya dakatar da tafiyar fasinjoji kimanin dubu 25.
Annobar guguwar wadda ta sako a ranar 3 zuwa 13 ga watan Maris na wannan shekarar, ta hana mutane sama da dubu 9 yin bulaguro, inda ta tirsasa Amurkawa milyan 2 rayuwa cikin duhu da kuncin rayuwa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng