Girma ya fadi: An gurfanar da wani dan shekaru 52 bisa laifin wasa da nonon kwaila

Girma ya fadi: An gurfanar da wani dan shekaru 52 bisa laifin wasa da nonon kwaila

Wani magidanci, Ajidare Oluwadare, mai shekaru 52 a duniya ya gurfana gaban kotun majistare dake Ikorodu a jihar Legas bayan samun an same shi da laifin wasa da nonon kwaila.

Dan sanda mai gabatar da kara, Saja John Iberedem, ya shaidawa kotun cewar wanda ake tuhumar ya aikata laifin ranar 26 ga watan Fabrairu da misalin karfe 4:00 na yamma.

Iberedem ya ce mutumin ya kira yarinyar yayin da take dawowa daga makaranta, ya ba ta wasu litattafai tare da shaida mata cewar zasu yi mata amfani, sannan ya ce ta dawo idan anjima domin karbar wasu litattafan.

Girma ya fadi: An gurfanar da wani dan shekaru 52 bisa laifin wasa da nonon kwaila
An gurfanar da wani dan shekaru 52 bisa laifin wasa da nonon kwaila

Bayan yarinyar ta koma ne sai ta sami mutumin babu komai jikinsa sai tawul iya kugunsa.

Babu kunya, ya jawo ta tare da shafa jikinta amma yarinyar tayi ta maza ta kubuce ta gudu gida ta sanar da iyayenta.

DUBA WANNAN: Zan yiwa Ganduje da duk masu taimkonsa a siyasance ritaya daga siyasa - Kwankwaso

Dan sandan ya ce laifin mutumin ya saba da sashe na 135(1) na kundin aikata laifuka na jihar Legas.

Wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin yunkurin cin mutuncin yarinyar.

Alkalin Kotun, F.A Azeez, ta bayar da shi beli a kan kudi, N200,000 da kuma shaidu guda biyu, sanan ta daga karar zuwa ranar 5 ga watan Afrilu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: