Wata mahaifiya ta bayar da diyar ta jinginar bashin N100 a jihar Ebonyi

Wata mahaifiya ta bayar da diyar ta jinginar bashin N100 a jihar Ebonyi

Wata mata mai sunan Veronica Igwe 'yar shekaru 38, ta bayar da diyar ta 'yar shekaru hudu, Uloma Igwe, a matsayin jinginar bashi na N100 da ta yi rance.

Misis Cecelia Elom, shugaba ta hukumar kula da kare hakkin yara yayin ganawa da manema labarai a birnin Abakaliki na jihar Ebonyi ta bayyana cewa, sun samu korafin wannan rashin sanin ciwon kai na Veronica a ranar Talatar da ta gabata.

Veronica dai ta bayar da 'yar cikin mai ta mai shekaru hudu a matsayin jingina ta bashin N100 da ta gaza sauke nauyin sa, wanda ya sanya mutane da dama ke tantama akan ko ita ta sha wahalar nakudar ta.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Veronica ta bayar da jinginar 'yar ta ga wata mata, Josephine Nwali dake bibiyar ta bashin N100 dake mazauniya ce a cikin jami'ar jihar Ebonyi dake birnin Abakaliki.

KARANTA KUMA: Dangote da Bill Gates sun kulla yarjejeniya da gwamnoni 6 akan allurorin riga-kafi

Tuni dai hukumar kula da kare hakkin yara ta yi ram da Josephine, inda kuma ta mika ta ga hukumar 'yan sanda ta jihar domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da ita a gaban kuliya.

Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar ICPC na neman taso keyar tsohon gwamnan jihar Filato Jonah Jang bisa laifin rashawa ta N5.6bn.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng