Hukumar ta kama haure da toron giwa na fiye da biliyan ciki wata biyu

Hukumar ta kama haure da toron giwa na fiye da biliyan ciki wata biyu

Ministan muhalli na kasa, Ibrahim Jibril, ya bayyana cewar, hukumar kwastam ta kama haure da toron giwa a Najeriya na kimanin biliyan N1.2bn tsakanin 15 ga watan Fabrairu da 22 ga watan Maris.

Ministan, da babban sakataren ma'aikatar, Shehu Ahmed, ya wakilta a wani taro da aka gudanar yau a Abuja a kan yadda za a dakile kasuwancin sassan dabbobin daji.

Hukumar ta kama haure da toron giwa na fiye da biliyan ciki wata biyu
Hukumar ta kama haure da toron giwa na fiye da biliyan ciki wata biyu

Hukumar kiyaye gandun daji ta WCS da hadin gwuiwar gwamnatin tarayya su ka gudanar da taron.

KU KARANTA: Muhimman Abubuwa 10 da ya kamata ku sani a kan sabon mataimakin gwamnan CBN

A ranar 15 ga watan Fabrairu, hukumar kwastam ta kama buhunhunan sassan giwa da aka yi kiyasin kudinsu zai kai miliyan N493,520,00, sannan cikin kasa da wata guda ta kara kama wasu sassan giwar da nauyinsu ya kai kilogram 8,492 da adadin kudi miliyan N732,520,00.

A wani labarin, Legit.ng ta sanar da ku cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Zamfara a yau, Alhamis, a cigaba da rangadin jihohin dake fama da kalubalen tsaro a Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar Buhari da tawagar sa sun dira a jihar da misalin karfe 10:40 na safiyar yau bayan tashinsu daga filin jiragen sama na Umaru Musa 'Yar'Adua dake jihar Katsina.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng