Bill Gates da Dangote sun sami kujera a yau Majalisar zartaswar Najeriya a Aso Rock

Bill Gates da Dangote sun sami kujera a yau Majalisar zartaswar Najeriya a Aso Rock

Tun zuwansa ziyarar aure a Najeriya, inda aka yi auren diyar abokinsa Dangote, Bill GAtes yana ta samun karramawa da zagayawa domin duba hanyoyi da zai taimakawa NAjeriya da ma zuba jari, tare da abokin nasa Aliko Gote

Bill Gates da Dangote sun sami kujera a yau Majalisar zartaswar Najeriya a Aso Rock
Bill Gates da Dangote sun sami kujera a yau Majalisar zartaswar Najeriya a Aso Rock

Tun zuwansa ziyarar aure a Najeriya, inda aka yi auren diyar abokinsa Dangote, Bill GAtes yana ta samun karramawa da zagayawa domin duba hanyoyi da zai taimakawa NAjeriya da ma zuba jari, tare da abokin nasa Aliko Gote.

A yau ne kuma hamshaqan masu hannu da shunin, suka zauna a majalisar tattalin arziki ta kasa karkashin Farfesa Yemi Osinbajo da dukkan gwamnonin kasar nan guda 36, domin aiki tare a fiddo hanyoyin da hamshakan zasu zuba jari.

DUBA WANNAN: Anyi dinar abinci da Bill Gates a Aso Rock, sun kuma yi yarjejeniya da gwamnoni 6

A taron kuma dai, akwai shugaban majalisar Dattijai da ta wakilai, shuwagabannin bankuna, Sarkin Kano SLS II, wasu mashawarta daga asusun agaji na Birtaniya da ma wasu masu fada aji a kasar nan.

Abubuwa da aka tattauna a taron, sun hada da, tattalin arziki, zuba jari, talauci da ma harkar noma da sama wa samari aikin yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng