Najeriya tana daya daga cikin kasashe mafi hadarin haihuwa a duniya - Bill Gates
Bill Gates, gawurtaccen attajirin nan na duniya kuma mai gidauniyar nan ta Bill and Melinda Foundation, ya bayyana cewa Najeriya tana daya daga cikin jerin kasashe mafi hadarin haihuwa a duniya.
Attajirin yake cewa Najeriya ta na wannan mataki ne a sakamakon kasancewar ta kasa ta hudu cikin jerin kasashen duniya dake fama da mace-mace a yayin haihuwa inda kasashen Sierra Leone, Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya da Chadi ke kan gaba.
Bill Gates ya bayyana hakan ne a yayin zaman majaliasar tattalin arzikin kasa da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Ya ci gaba da cewa, babban ofishin gidauniyar sa a nahiyyar Afirka yana Najariya wanda kawowa yanzu ya sadaukar da fiye da Dala Biliyan 1.6 tare da manufa ta kara inganta sadaukawar sa a kasar.
KARANTA KUMA: Gwamnatin Kasar Birtaniya ta bayar da agajin magunguna na N780m ga jihar Kano
Ya kara da cewa, Najeriya tana da matukar ci gaba ta fuskar tattalin arziki mai girman gaske sai dai tasirin hakan yana da nasaba ne da shawarwari da tsare-tsaren shugabannin ta.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Dangote da Bill Gates sun kulla wata yarjejeniya da gwamnoni 6 na yankin Arewa wajen wadatar da allurorin riga-kafi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng