Bincike: An gano wani yaro guda daya daga cikin yan matan Dapchi da yan Boko Haram suka sako
Bincike daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da samuwar wani karamin yaro a cikin yan matan Dapchi guda 104 da kungiyar ta’addanci ta sako a ranar Laraba 21 ga watan Maris.
Rahotannin da Legit.ng ta samu daga fadar shugaban kasar ta tabbatar da cewa sunan wannan karamin yaro Mala, kuma yana da ne ga wani Malami dake koyarwa a kwalejin yan matan dake garin Dapchi.
KU KARANTA: Cigaba da riƙe wata dalibar Dapchi saboda kin shiga addinin Musulunci: Bala Lau ya mayar da martani
Majiyar Legit.ng ta ruwaito har da wannan yaro mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka tattara tare da yan mata 110 suka yi awon gaba da su a ranar 19 ga watan Feburairu.
Idan za’a tuna, yan ta’addan sun far ma sakandarin kimiyya na yan mata ne dake garin Dapchi da misalin karfe 10 na safiyyar ranar 19 ga watan Feburairu a lokacin da daliban ke hutun tara, inda suka dinga harbe harbe a sama, har sai da suka kammala dauke yan matan.
Sai dai kimanin wata guda a da sace yan matan, kuma sakamakon wata tattaunawa da gwamnati ta shiga da kungiyar, an samu nasarar shawo kan kungiyar, inda ta yarda ta dawo dasu da kanta har garin Dapchi, ba tare da bukatar kudi ko musayar fursuna ba, kamar yadda gwamnati ta tabbatar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng