Babu sharadi babu ko kwabo Boko Haram ta sako yan matan Dapchi – Garba Shehu
A ranar Laraba 21 ga watan Maris ne mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka sako wasu daliban sakandarin kimiyya na garin Dapchi a jihar Yobe, bayan kimanin wata guda a hannunsu.
Gwamnatin tarayya ta bayyana rawar da ta taka ta bakin mashawarcin shugaban kasa kan harkar watsa labarai, Garba Shehu wanda ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta taka muhimmin rawa a kokarin ceto yan matan.
KU KARANTA: Barawon da ya sace biliyan 33 na yan fansho ya dawo da biliya 23 tare da fuskantar shekaru 6 a Kurkuku
Garba ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da gidan rediyon BBC Hausa, inda yace a baya kungiyar ta dauki alkawarin ba zata sake satar mutane ba, inda yace amma sai gashi a wannan karon sun karya alkawarinsu ta hanyar satar yan matan Dapchi.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Garba ya tabbatar da tattunawa tsakanin wakilan gwamnatri da wakilan yan ta’addan, sa’anann ya musanta batun cewa wai gwamnati ta biya kudin fansa, inda yace gwamnati bata biya ko kwabo ba, kuma ba ta yi musayar yan ta’adda dake hannunta da Boko Haram ba.
“Alkawari suka dauka cewar ba zasu sake satar mutane ba, don haka bayan sace yan matan Dapchi sai wakilan gwmanati dake tattaunawa dasu suka tuna musu wannan alkawari, daga nan ne sai yan Boko Haram suka tabbatar da alkawarin, sa’annan suka dauki alwashin mayar da yan matan don tsayawa akan wannan alkawari.” Inji shi.
Sai dai Garban yace a lokacin da yan ta’addan zasu shiga garin Dapchi, gwamnati ta umarci Sojojin Najeriya su tsagaita wuta, don su baiwa yan ta’addan damar shiga garin tare da mayar da yaran makarantarsu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng