Sama da mutum 100,000 suka yi kaura daga jam'iyyar PDP da APC zuwa jam'iyyar SDP

Sama da mutum 100,000 suka yi kaura daga jam'iyyar PDP da APC zuwa jam'iyyar SDP

- Sauya jam'iyya dai ga 'yan siyasar Najeriya ba abu bane sabo, sai kaga yau wannan ya bar jam'iyyar shi da aka san shi ya koma wata, a jiya ne kimani mutum 100,000 a jihar Adamawa suka yi kaura daga jam'iyyoyin APC da PDP suka koma jam'iyyar SDP

Sama da mutum 100,000 suka yi kaura daga jam'iyyar PDP da APC zuwa jam'iyyar SDP
Sama da mutum 100,000 suka yi kaura daga jam'iyyar PDP da APC zuwa jam'iyyar SDP

Sama da mutane 100,000 ne a jihar Adamawa suka bar jam'iyyar PDP da APC mai mulki suka koma sabuwar jam'iyyar SDP.

Shugaban jam'iyyar SDP, Cif Olu Falae, shi ya sanar da hakan a jiya lokacin da jam'iyyar ta ke bikin karbar Cif Emmanuel Bello, wanda yayi kaura ya dawo jam'iyyar jiya a garin Yola.

DUBA WANNAN: An kama wani matashi a jihar Zamfara yana sayar da kudin bogi

"Na zo na karbi Cif Emmanuel Bello da kuma mutane 100,000 wanda suka canja sheka daga jam'iyyar APC mai mulki da kuma jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar mu mai albarka ta SDP, daga yau sun zama cikakkun 'yan jam'iyyar SDP," inji shugaban jam'iyyar.

Ya ce jam'iyyar SDP ta jima a kasar nan, jam'iyyar ta yi shiru ne tun lokacin da marigayi Abiola da Babagana Kingibe suka barta a shekarar 1993.

Shugaban jam'iyyar na kasa, Farfesa Jerry Gana, ya ce wannan ita ce fita ta farko da suka yi a wannan shekarar, inda ya kara da cewar jam'iyyar tana maraba da duk wanda yake sha'awar shigowa cikin ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng