Jama'a sun sa alamar tambaya game da dawo da 'Yan Makarantar Dapchi

Jama'a sun sa alamar tambaya game da dawo da 'Yan Makarantar Dapchi

- Bayan kusan wata guda ne da sace Matan Dapchi aka maido su gida

- An sasanta da Boko Haram sun maido 'Yan makaranta sama da 100

- An hana Jami'an tsaro shiga Garin na Dapchi domin daukan rahoto

- Wasu 'Yan makaranta 5 an ce sun rasu daga cikin yaran da aka sace

A jiya ne da sasssafe 'Yan Boko Haram su ka lallaba su ka dawo da 'Yan matan Makarantar Garin Dapchi da su ka sace kusan wata guda da su ka wuce. Dama kafin nan manyan Jamia'an tsaro sun tabbatar da cewa matan sun kusa dawowa.

Jama'a sun sa alamar tambaya game da dawo da 'Yan Makarantar Dapchi
'Yan Matan Dapchi lokacin da su ka dawo gida cikin amana

Sai dai wasu sun sa alamar tambaya game da abin da ya faru. Babban 'Dan adawar wannan Gwamnatin Gwamnan Jihar Ekiti watau Ayo Fayose ya bayyana cewa wadanda su kayi sanadiyar sace 'Yan Makarantar su ne su ka dawo da su ba wasu ba.

KU KARANTA: 'Yan matan Dapchi za su gana da Shugaban kasa Buhari

Wani 'Dan Jarida a Amurka Jackson Ude yace da-walakin a wannan batun ganin yadda 'Yan Boko Haram su ka maido yaran Makarantar cikin tsabta da ban sha'awa har da kayan guzurin su kuma salin-alin ba tare da kutsowar Jami'an tsaro ba.

Gwamnati dai ta hana 'Yan jarida su shiga Garin Dapchi su dauki rahoto. Bayan an ajiye yaran dai an yi maza ne an wuce da su Birnin Tarayya Abuja. Mutanen Gari dai sun fito su na murna da cashewa da 'Yan ta'adda lokacin da aka maido masu yaran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng