Fiye da 'yan jam'iyyar APC da PDP 100, 000 sun sauya sheka zuwa SDP a jihar Adamawa

Fiye da 'yan jam'iyyar APC da PDP 100, 000 sun sauya sheka zuwa SDP a jihar Adamawa

Da sanadin jaridar Daily Trust mun samu labarin cewa, fiye da mambobi dubu dara na jam'iyyun APC da PDP sun sauya sheka zuwa zuwa jam'iyyar SDP (Social Democratic Party) a jihar Adamawa.

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban jam'iyyar na kasa; Cif Olu Falae, ya bayyana hakan a yayin sauyin shekar mambobin a gidan Silima na Lamido dake jihar Adamawa.

Olu Falae yake cewa, jam'iyyar SDP ta kasance da kafuwa tun a shekarar 1982 a lokacin gwamnatin Abiola da Kingibe.

Legit.ng ta fahimci cewa, mambobin da suka sauya sheka sun fito daga kimanin kananan hukumomi 25 na jihar.

KARANTA KUMA: Majalisar Wakilai ta sake hurawa Buhari wuta kan dokar sauya jadawalin zabe da kafa hukumar Peace Corps

Daya daga cikin shugabannin jam'iyyar, Farfesa Jerry Gana ya bayyana cewa, wannan alamu da yake nuna irin ci gaban da jam'iyyar ke samu a kasar nan.

Jaridar ta Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugabannin jam'iyyar APC da jiga-jigan ta na majalisar dattawa sun shiga ganawa a yau Laraba domin warware matsalolin da jam'iyyar ke fuskanta a sakamakon gabatowar zaben kasa na 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng