Saraki yayi sharhi akan sakin yan matan Dapchi

Saraki yayi sharhi akan sakin yan matan Dapchi

- Bukola Saraki ya taya shugaban kasa Buhari murna kan sakin yan matan Dapchi

- Shugaban majalisar dattawan yace yana fatan zasu sake haduwa da iyayensu nan bada jimawa ba

- Ya bukaci a bari su koma makaranta

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki yayi martini ga sakin wasu daga cikin yan matan Dapchi a jihar Yobe bayan yan Boko Haram sun sace su.

Da farko Legit.ng ta rahoto cewa yan ta’addan sun saki yan matan a ranar Talata, 21 ga watan Maris.

Da yake sharhi, Saraki ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar sakin yan matan.

Ya bukaci gwamnatin jihar Yobe da iyayen yaran su tabbatar da cewa sun koma makaranta.

KU KARANTA KUMA: Hotunan yan matan makarantar Dapchi da aka saki sun bayyana

Daga karshe yace yana fatan zasu sake haduwa da iyayensu nan bada jimawa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng