Sarakuna sun taya al’umman Dapchi murna kan sakin yan matan da aka sace
Kungiyar sarakunan Anambra ta tsakiya ya taya al’umman Dapchi dake jihar Yobe farin ciki kan sakin wasu daga cikin yan matan makarantar yankin da aka sace.
Shugaban kungiyar, Igwe Chukwuemeka Ilouno, ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya yayinda yake martini kan sakin yan matan da akayi a safiyar ranar Laraba.
NAN ta ruwaito cewa ministan bayanai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa an dauki bayanai akan yan matan 76 da aka saki.
Basaraken wanda ya kasance sarkin masarautar Ifitedunu dake Anambra ya roki gwamnatin tarayya da ta yi kokarin ganin an saki sauran yan matan.

Ilouno ya bayyana cewa yan Najeriya na zuba ido domin samun cikakken bayani kan yadda gwamnati tayi wannan gagarumin nasara.
KU KARANTA KUMA: Hukumar kwastam ta kama kayayyaki na N2.55b
A baya Legit.ng ta rahoto cewa wani hoto mai ban mamaki ya billo bayan sakin yan matan makarantar Dapchi da Boko Haram suka yi.
A cikin hoton an nuno al’umman garin Dapchi na dagawa yan ta’addan hannu a yayinda suke kokarin barin garin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng