Hotunan mazauna garin Dapchi yayinda suke daga ma yan ta’addan Boko Haram hannu lokacin da suke barin garin
Wani hoto mai ban mamaki ya billo bayan sakin yan matan makarantar Dapchi da Boko Haram suka yi.
A cikin hoton an nuno al’umman garin Dapchi na dagawa yan ta’addan hannu a yayinda suke kokarin barin garin.
Ga hotunan a kasa:
A baya mun kawo cewa cewa yan kungiyar Boko Haram sun saki yan matan Dapchi.
Rahoto ya kara da cewa sun mayar da su garin Dapchi amma an samu karamin akasi, biyar daga cikin yan matan sun rasa rayukansu.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Adamawa ta yaba ma sakin yan matan makarantar Dapchi da akayi
Shugaban kwamitin iyayen yan matan Dapchin, Bashir Manzo, ya tabbatar da cewa an dawo da yan matan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng