Nayi murna da farin ciki sosai game da sakin 'yan matan Dapchi - Mama Boko Haram

Nayi murna da farin ciki sosai game da sakin 'yan matan Dapchi - Mama Boko Haram

A yau Laraba ne wata mai kare hakkin bil adama, Aisha Wakil wanda akafi sani da 'Mama Boko Haram' ta bayyana farin cikin ta game da sakin yan matan makarantar sakandire na Dapchi da Boko Haram suka sace kwanakin baya.

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta sanar da cewa yan ta'addar kungiyar na Boko Haram sun sako yan matan na Dapchi a ranar 19 ga watan Fabrairun 2018.

Nayi murna da farin ciki sosai game da sakin 'yan matan Dapchi - Mama Boko Haram
Nayi murna da farin ciki sosai game da sakin 'yan matan Dapchi - Mama Boko Haram

Wakil ta shaida wa NAN cewa tayi matukar farin ciki yayin da ta samu labarin cewa an sako yan matan na Dapchi.

KU KARANTA: Yadda wani mutum a Nasarawa ya jefa diyar sa a rijiya bisa zargin maita

"Nayi matukar murna da farin ciki bisa sako yan matan, wannan gagarimin cigaba ne," inji ta.

A baya, NAN ta ruwaito wani labari inda Wakil ta bayyana sha'awar taimakawa wajen yin sulhu da yan ta'addan don ganin an sako yan matan lafiya.

Hakazalika, Shugaban kungiyar daliban yara na makarantar sakandire na Dapchi, malam Bashir Manzo shima ya bayyana farin cikin sa game da sako yan matan.

Manzo ya ce a halin yanzu suna tattance adaddin yan matan ne kuma wasu daga cikin su sun tafi gida tare da iyayen su.

Suma shugabananin kungiyar iyayen ya makarantar Sakandire na Chibok, Mr. Maina Musa da Ayuba Alamson sun bayyana farin cikin su game da sako yan matan na Dapchi.

Sun kuma kara da mika roko ga gwamnatin tarayya ta taimaka don ganin dukkan yan matan da ke tsare a wajen yan kungiyar ta Boko Haram sun dawo wurin iyayen su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164