Gwamnatin Adamawa ta yaba ma sakin yan matan makarantar Dapchi da akayi
Gwamnatin Adamawa ta nuna farin ciki kan sakin yan matan makarantar Dapchi da Boko Haram suka yi.
Da yake magana ga manema labarai kan ci gaban, kwamishinan bayanai Ahmad Sajoh yace labara ne mai dadi ga gwamnatin.
Haka zalika da yake magana dan majalisa mai wakiltan mazabar Michika/Madagali, Adamu Kamale yace ya ji dadin ci gaban wanda ya bayyana a matsayin “Allah ya amsa addu’o’inmu.”
Wasu dalibai da akayi hira dasu sun nuna jin dadinsu kan lamarin sannan sun bukaci gwamnati da ta dauki mataki domin guje ma sake afkuwar haka.
KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar APC da jami'an gwamnatin tarayya na tsoratar da likitoci na - Metuh
A baya Legit.ng ta rahoto cewa yan kungiyar Boko Haram sun saki yan matan Dapchi.
Rahoto ya kara da cewa sun mayar da su garin Dapchi amma an samu karamin akasi, biyar daga cikin yan matan sun rasa rayukansu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng