'Sauran kiris na zauce yayin da na kama uwargida na ta na tarawa da wani mutum'
Wani direba Mista Nurudeen Babalola, ya yi karar mai dakin sa Fatima Babalola har gaban kotun al'adu ta Oja-Oba dake babban birnin Ibadan na jihar Oyo, inda yake neman kotun ta salwantar da auren su a sakamakon keta ma sa haddi.
Nurudeen ya shaidawa kotun cewa, sauran kiris ya zauce yayin da ya cafke matar sa ta na tarawa da wani mutum a gadon mahaifiyar ta, kuma surukar ta sa ta tabbatar ma sa da cewa ai daduron 'yar ta ne.
Bayan kwana guda da wannan magidanci ya cafke uwargidan sa tana aika-aika, sai ta kwashi kafafu ta kama gabanta.
Sai dai a na ta jawabin, Fatima ta shaidawa kotun cewa batutuwan mai gidan ta ba wani abu da ya wuce shaci fadi da karairayi marasa tushe.
KARANTA KUMA: Dalilin da yasa har yanzu ba bu ci gaba a yankin Neja Delta
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Alkalin Kotun Ademola Odunade, ya salwantar da wannan aure inda ya baiwa Nurudee dama ta ci gaba da dawainiya da 'ya'yan su biyu.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar Sojin kasa ta karya ikirarin kungiyar Amnesty International na cewar an ankarar da hukumomin tsaro kafin afkuwar harin 'yan Matan Dapchi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng