Fusatattun matasa sun kona barawon waya a jihar Nasarawa
- Wani barawon waya a jihar Nasarawa ya gamu da fushin matasa a ranar Litinn
- Fustattun Matasa sun babbaka wani barawon waya a jihar Nasarawa
Dubun wani barawon waya ta cika yayin da ya gamu da fushin matasa lokacin da yake kokarin sace wayar wata mata mai dauke da juna biyu.
Matasan sun lakadawa barawon dukan tsiya sannan suka banka mu shi wuta ya kone kurmusu.Wannan mumunar al’amari ya faru ne a ranar Litinin a garin Mararaba Gurku dake jihar Nasarawa.
Wani da abin ya faru a gaban sa mai suna, Martins Ago, ya fadawa manema labaru cewa an kama barawon wayar ne a lokacin da yake kokarin ya fizge wa wata mata Jakarta a lokacin da ta fito daga cikin wani banki.
KU KARANTA : An kama dala miliyan $9m a gidan tsohon shugaban hukumar shirin Amnesty, Paul Boroh
Da barawon ya kasa fizge jakar da hanun matar sai ya nusheta ta fadi daganan sai ta fara ihu .Kafin a ce tak mutane sun yi ram da shi suka dunga jibgar sa har saka masa taya suka babbake shi a wurin.
Naushin da yayiwa matar yayi sanadiyar mutuwar mata bayan wani dan lokaci.
Dannan wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng