Yadda wani mutum a Nasarawa ya jefa diyar sa a rijiya bisa zargin maita
- Wani mutum dan shekara 30, mai suna Manu Yakubu, ya gurfana a gaban kotun jihar Nasarawa, bisa laifin jefa ‘yarsa rijiya
- Yakubu, mazaunin unguwar Gidigidi ne, a jihar, an zargeshi da laifin jefa ‘yarsa cikin rijiya da gangan bisa zargin da yake mata na maita
- Mai gabatar da kara ‘Yan Sanda, James Anata, ya bayyanawa kotu cewa, Yakubu, aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Disamba, shekara ta 2017
Wani mutum dan shekara 30, mai suna Manu Yakubu, ya gurfana a gaban kotun jihar Nasarawa, bisa laifin jefa ‘yarsa rijiya da gangan. Yakubu, mazaunin unguwar Gidigidi ne, a jihar, an zargeshi da laifin jefa ‘yarsa cikin rijiya da gangan bisa zargin dayake mata na maita
Mai gabatar da kara, James Anata, ya bayyanawa kotu cewa, Yakubu ya aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Disamba, shekara ta 2017. A sauraron karar da a kayi a ranar Talata, wani mai bayar da shaida, Samuel Kuje, ya fadawa kotu cewa, ya gano yarinyar ne a cikin rijiyar dake gonarsa a ranar 8, ga watan Disamba, da safe.
KU KARANTA: Muna bukatar amincewar Buhari kafin janye jami’an 'Yan sanda da ke gadin manyan mutane - Sifeta Idris
Yace, “Daga farko ya dauka Aljana ce, sai bayan ya tambayeta ko wacece ita, tace masa Jenifa Ayuba daga Gidigidi”. Yace, “Daga nan na ruga zuwa Gidigidi dan in shidawa Mai Gari, Mista Ashila da wasu mutane hudu; muka koma gonar tawa inda rijiyar take muka fito da yarinyar daga ciki; Daga nan sai na kira jami’an ‘Yan Sanda daga B division a garin Lafia don su kama mai laifin.”
Dan Sandan yace, Yakubu, ya amsa laifinsa na jefa yarinyar rijiya bisa zarginta da zama daya daga cikin ‘yan kungiyar asiri, kuma itace sanadiyar matsalolin dake damunsa. Yakubu, kuma ya rubuta a bayanin daya yiwa hukumar ‘Yan Sanda, cewa yarinyar ta bayar dashi da matarsa ga ‘yan kungiyar tasu don a kashesu.
Ya kara da cewa, yarinyar mai shekaru shida, ta amsa masa cewa, itace tayi sanadiyar mutuwar kawunta, Diour Adamu, da kannenta biyu da suka rasu bayan haihuwarsu bada jimawa ba, kuma ta kan fita ta shiga daji tayi sama da mako daya sannan ta dawo.
Mai gabatar da karar, a ranar Talata, ya bukaci mai shari’a da ta hukunta Yakubu, bisa laifin da ake zarginsa, dangane da tabbacin da hukumar ‘Yan Sanda ta bayar kan laifin da ya aikata.
Mai shari’a, Rose Fuji, ta daga sauraron karar zuwa 23 ga watan, Afirilu, 2018.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng