Kwararan hujjoji guda 5 da zasu kai Buhari ga nasara a zabukan 2019
Wani bincike ya bayyana cewar a yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari na jiran ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2019 ne kawai domin a rantsar da shi a karo na biyu, don kuwa dukkanin alkalumma sun tabbatar da yaci zabe y agama, tun kafin a fafata.
Jaridar Pulse ce ta gudanar da wannan bincike, inda ta kawo hujjojin guda biyar da suka kunshi:
1- Yawan sababbin masu kada kuri’a
Alkalumman daga hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta fitar sun bayyana adadin yan Najeriya da suka yi rajistan zabe sun kai miliyan 73, 944, 312, inda daga cikin wannan adadin akwai mutane miliyan 18,505,984 daga yankin Arewa maso yamma, yayin da yankin Kudu maso gabas keda miliuan 8,293,093.
Arewa ta tsakiya na da miliyan 10,586,965, Arewa maso gabas 9,929,015, Kudu maso yamma 14,626,800, sai kudu maso kudu dake da miliyan 11,101,193. Don haka duba da wadannan alkalumma, ya nuna cewar yankunan da APC ke da karfi sun fi yawan sabbin masu kada kuri’u.
KU KARANTA: Yadda wasu marasa Imani suka watsa ma wata kyakkyawar budurwa ruwan ‘Acid’ bayan sun yi mata fyade
2- Rashin adawa
Zuwa yanzu a iya cewa jam’iyyar PDP da ake yi ma kallon jam’iyyar adawa ta gaza taka rawar data rawar da ake tsammani daga gareta, na zama ma jam’iyyar APC mai mulki tarnaki a duk lokacin da ta kauce hanya.
Wannan rashin lakka na jam’iyyar PDP baya rasa nasaba da mummunan kayen da ta sha a hannun jam’iyyar APC a shekarar 2015, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kayar da shugaban kasa mai ci, Goodluck Jonathan, don haka har yanzu basu farfado daga doguwar sumar ba.
3- Soyayyar Buhari
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wata ziyara da Buhari ya kai jihar Kano, inda wakilinta yace har sai da y adage tagogin motarsa don gudun kada jama’a su afka masa duba da kamanninsa dake nuna shi bad an Arewa bane.
Rahoton ta bayyana cewa a duk jihar da Buhari ya ziyarta a Arewa, zaka hangi dafifin mutane da suka fitar farin dango don tarbarsa, suna kirarin ‘Sai Baba’, musamman ma idan ya daga musu hannu, kamar yadda ya saba.

4- Sauyin sheka zuwa APC
A yanzun nan jam’iyyar APC na da jihohi 24 a hannunta gam gam! Wanda hakan ke nufin ta dara jam’iyyar PDP dake da jihohi 11, da kuma jam’iyyar APGA dake da jiha guda 1.
Sai dai tagomashin jam’iyyar APC bai tsaya ba bayan lashe zaben 2019, inda gagga gaggan yayan jam’iyyun adawa da suka hada da PDP, APGA, LP suka dinga afkowa cikin jam’yyar APC domin a dama dasu. A taikace ma ana iya ganin APC zata sake kwace wasu jihohi daga hannun PDP.
5- Yaki da cin hanci da rashawa
Yakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi da cin hanci da rashawa, wanda hakan yayi sanadiyyar kama tsoffin manyan jiga jigan gwamnatin da ta shude, tare da gurfanar dasu gaban Kotu, inda a yanzu ake jiran hukuncin Kotun, hakan ya kara ma gwamnatin Buhari sahihanci.
Da wannan ake ganin da dama daga cikin yan Najeriya zasu goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari don ya cigaba da zama fargaba ga barayin gwamnati.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng