'Marigayi Sanata Wakil ya nemi uwargidan sa ta bashi Shayi kafi ajali ya katse ma sa hanzari'

'Marigayi Sanata Wakil ya nemi uwargidan sa ta bashi Shayi kafi ajali ya katse ma sa hanzari'

A yayin da majalisar wakilai ta dakatar da zamanta na ranar yau Talata domin jimamin rasuwar marigayi Sanata Ali Wakil, wani dan majalisar Mista Muhammad Sani Abdu ya bayyana yadda ajali ya katse hanzarin babban aminin sa.

Marigayi Sanata Ali Wakil ya shirya tsaf domin kama hanyar sa ta zuwa birnin Yola na jihar Adamawa wajen halartar daurin aure na diyar babban sakataren gwamnatin tarayya na kasa, Mista Boss Mustapha.

Sai dai kafin barin gida, marigaya Wakil ya umarci uwargidansa ta nema ma sa abin sanyawa a baka kamar yadda Sani Abdu ya bayyana a farfajiyar majalisar dokoki ta tarayya.

'Marigayi Sanata Wakil ya nemi uwargidan sa ta bashi Shayi kafi ajali ya katse ma sa hanzari'
'Marigayi Sanata Wakil ya nemi uwargidan sa ta bashi Shayi kafi ajali ya katse ma sa hanzari'

Ya ci gaba da cewa, "a yayin da uwargidan sa ta kawo wa mijin na ta Fate, sai yace yafi son abinci marar nauyi kuma ya nemi da tayi hakuri ta kawo ma sa ruwan Shayi."

"A yayin dawowar ta da kofin Shayi ne ta riski gawar mai gidan ta wanwar a kasa, wanda wannan umarni shine ganawar su ta karshe da shi."

Dan majalisar a yayin bayyana wa abokan aikin sa yadda ajali ya riski aminin sa, ya kuma hikaito yadda ya wanke gawar sa kuma ya hada ta domin kai ta zuwa makwanci.

KARANTA KUMA: Bincike: Jerin jihohi 8 mafi kantar bashi a Najeriya

A yayin daukar gawa, Dan majalisa Sani Abdu ya nemi ko uwargidan marigayi ko tana da bukatar sake sanya fuskar mijin ta a idanu, kuma ta amsa da na'am cikin jarumta ba tare da tsoron gawa ba irin na mata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, sai da mata suka taru wajen kwakwule uwargidan daga jikin mijin ta wanda nan take ta fadi sheme a sume da har sai da ta sha yayyafi na ruwa.

Legit.ng ta fahimci cewa, Mista Yakubu Dogara wanda ya kasance ya fito daga mazaba daya da marigayin da kuma Sani Abdu, shine ya dakatar da zaman majalisar zuwa ranar gobe Laraba bayan an kammala addu'o'i ga mamacin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: