Shugaba Buhari ya shiga ganawa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirrance tare da tsohon mataimakin shugaban kasa, Muhammad Namadi Sambo a fadar Villa dake garin Abuja.
Jaridar The sun ta ruwaito cewa wannan ganawar ta dauki tsawon minti 25 a ofishin shugaban kasa tare da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya shaidawa manema labarai na fadar shugaban kasa cewa, ganawar sirri ce tsakanin sa da shugaba Buhari, wanda daga bisani ya kama gaban sa cikin motar sa da misalin karfe 12.25 na ranar yau Talata.
Legit.ng ta fahimci cewa, tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi makamanciyar wannan ganawa ta sirri da Farfesa Yemi Osinbajo a watan Mayu na shekarar da ta gabata a yayin da yake mukaddashin shugaban kasa.
KARANTA KUMA: Bincike: Jerin jihohi 8 mafi kantar bashi a Najeriya
Rahotanni sun bayyana cewa, Namadi ya kuma halarci sallar Juma'a tare da shugaban kasa Buhari a fadar sa ta Villa tun a watan Satumba na shekarar da ta gabata a yayin bikin cikar shekaru 57 na samun 'yancin kai da Najeriya ta yi.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani jami'in dan sanda ya harbe jami'in soji ana tsaka da cacar baki a jihar Delta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng