Kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta nemi shugaba Buhari ya mike tsaye kan jagorancin Najeriya
Kungiyar JNI (Jama'atu Nasril Islam) karkashin jagorancin Sultan na Sakkwato, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya tashi daga gyan-gyadin sa wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma a fadin kasar nan.
Wannan kira a cewar kungiyar ya zamto wajibi ne a sakamakon kashe-kashe da zubar da jinin al'umma da makiyaya ke ta faman aiwatar wa musamman a kauyen Bassa na jihar Filato a kwana-kwanan nan.
Kakakin kungiyar Dakta Khalid Abubakar Aliyu, shine ya bayyana hakan a wata ganawar ranar Litinin din da ta gabata da manema labarai a garin Kaduna.
Kungiyar ta yi Allah wadai da afkuwar harin da ya salwantar da rayuka da dama tare da asarar mahallai da suka haura 150 a jihar ta Filato.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa kungiyar ta gargadi hukumomin tsaro akan tayar da tarzoma wajen goyon bayan kowane bangare a jihar Filato da sauran sassa a kasar nan.
KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Attahiru Bafarawa da iyalansa sun halarci bikin yaye dalibai na dan sa a birnin Landan
Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyar JNI ta kuma nemi hukumomin tsaro akan kada suke rangwantawa duk wani mai hannu cikin wannan hare-hare, inda ta lcewa dole sai hukumomin tsaro sun kara kwazo wajen damko masu wannan ta'addanci domin fuskantar fushin doka.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar 'yan sanda ta yi karin haske kan barazanar da kiwo ke haddasawa fulani a kasar nan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng