'Yan Shi'a sunyi tattaki domin tunawa da ranar mutuwar Shaikh Qasim Umar Sokoto

'Yan Shi'a sunyi tattaki domin tunawa da ranar mutuwar Shaikh Qasim Umar Sokoto

- Tun lokacin da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama shugaban 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi wato shi'a a Disambar shekarar 2015, tunda ga lokacin 'yan kungiyar suke ta fafutukar ganin an sako shugaban nasu, ta sanadiyyar haka ne shugaban kungiyar na shiyyar jihar Sokoto ya rasa ransa, a lokacin da suka fito zanga - zanga a Abuja kwanaki 40 da suka wuce

'Yan Shi'a sunyi tattaki domin tunawa da ranar mutuwar Shaikh Qasim Umar Sokoto
'Yan Shi'a sunyi tattaki domin tunawa da ranar mutuwar Shaikh Qasim Umar Sokoto

'Yan kungiyar 'yan uwa musulmi na Najeriya wato (Shi'a) sun kaddamar da wani tattaki na zaman lafiya na tunawa da ranar mutuwar jagoran kungiyar na jihar Sokoto Shaikh Qasim Umar, wanda yau yayi kwana 40 da mutuwa.

DUBA WANNAN: Trump ya nemi tallafin kudi a wurin kasar Saudiyya

Qasim Umar ya rasa ransa sanadiyyar harsashin daya taba shi a watan Janairu, lokacin da yake jagorantar 'yan kungiyar akan zanga-zangar da suke ta neman a sakan musu shugaban su Shaikh Ibrahim Zakzaky, wanda hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama a watan Disambar shekarar 2015.

'Yan shi'ar wanda suka tako daga kan titin Unity Fountain zuwa babbar Sakatariya ta tarayya dake Abuja, sunce, kashe Shaikh Qasim Umar da aka yi, hakan ya nuna irin mulkin kama karya da gwamnatin kasar nan take yi.

S.I. Ahmed wanda yayi magana da yawun kungiyar, ya nuna rashin jin dadin shi akan halin da shugaban nasu yake ciki na rashin isashiyar lafiya. inda ya kara da cewar gwamnatin Najeriya zata dauki alhaki idan har wani abu ya faru dashi.

"Ya kamata al'ummar Najeriya dama duniya baki daya su san cewar ba a kama Shaikh Zakzaky da laifin komai ba, saboda haka daure shi da aka yi, yana nuni da cin zarafi da kuma keta haddin shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng