Hukumar DSS ta bayana yadda ta kama wani shahararren mai safarar makamai a Najeriya
- Hukumar DSS ta bayyana yadda ta cika da wani shararren mai safarar makamai a jihar Taraba
- DSS ta ce ta kwashe shekaru goma ta na neman mai safarar bindigogin da ta kama
Rundunar hukumar tsaro na farin kaya (DSS), ta ce, ta kama wani shahararen mai safarar bidigogi a Najeriya mai suna Jonah Abbey, wanda sunan sa ke cikin jerin sunayen mutanen da jami’an tsaro kasar ke nema ruwa a jallo.
Hukumar DSS ta ce, ta kwashe shekaru goma ta na neman Jonah Abbey wanda aka fi sani da Jonah IDI, ruwa a jallo.
Ana zargin mai lafin da sayar wa kungiyoyi masu tada kayar baya da 'yan ta'ada fadin kasar muggan makamai.
KU KARANTA : Mamora yaki karban sabuwar mukamin da Buhari ya bashi
A wata sanarwa da hukumar DSS ta fitar a ranar Lahadi, ta ce jami’anta sun yi aiki sosai a cikin kwana goma da suka gabata inda suka kama masu aikata manyan laifi da dama kasar cikin kawai masu garkuwa da mutane, masu safarar bindigogi da masu satan shanu
A sanarwar da hukumar DSS ta fitar a ranar 13 ga watan Maris da misalin 12.20 na rana ta ce ta yi nasarar kama, Mista Abbey, tare da direban sa, Agyo, a garin Wukari dake jihar Taraba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng