Sirrin boye: Kungiyar hadakar Obasanjo na shirin fito da Kwankwaso takara a 2019

Sirrin boye: Kungiyar hadakar Obasanjo na shirin fito da Kwankwaso takara a 2019

Muhimman bayani na ta kara bayyana a filin game da manufofin hadakar nan da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya kafa a baya da nufin abun da ya kira dora kasar Najeriya akan turba daidaitatta.

Hakan ya kara fita fili ne biyo bayan wani taron sirri da majiyar mu ta ruwaito cewa an gudanar da wasu jiga-jigan tafiyar hadakar a garin Legas inda aka ce sun aika da goron gayyatar su zuwa ga tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Sirrin boye: Kungiyar hadakar Obasanjo na shirin fito da Kwankwaso takara a 2019
Sirrin boye: Kungiyar hadakar Obasanjo na shirin fito da Kwankwaso takara a 2019
Asali: Facebook

KU KARANTA: Karya ne ban gana da Obasanjo ba - Kwankwaso

Legit.ng ta samu cewa duk da dai har yanzu takamaimai ba'a san abun da aka tattauna ba, amma masu sharhi akan lamurran siyasa na ganin batun bai rasa nasaba da zaben 2019 da ke tafe musamman ma dai ganin cewa shi Sanata Kwankwaso din yana da alaka ta musamman da Cif Obasanjo.

A wani labarin kuma, Shugabannin jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) da sauran masu ruwa da tsaki sun soma wani shirin sasanta bangaren zartarwa da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta da kuma bangaren 'yan majalisu da Sanata Bukola Saraki ke jagoranta.

Wannan dai matakin da suka dauka kamar yadda muka samu ya biyo bayan takun sakar da yanzu haka ake samu tsakanin bangarorin biyu musamman ma wajen tirka-tirkar sauya jadawalin zabe mai zuwa inda 'yan majalisun suka sha alwashin zartar da dokar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng