Tawagar Gwamnatin Tarayya ta isa Bauchi domin ta'aziyyar Marigayi Sanata Wakili
- Gwamnatin Tarayya ta kai wa mutanen Bauchi ziyarar ta’aziyya
- A jiya kwatsam Sanatan Bauchi na Kudu watau Ali Wakili ya rasu
- Shugaba Buhari ya aikawa Jama’a ta’aziyyar ‘Dan Majalisar Jihar
Tawagar Gwamnatin Tarayya ta kai ziyarar makoki na Marigayi Sanatan Kudancin Jihar Bauchi Ali Wakili domin yi masu ta’aziyya.
A jiya ne kwatsam Ali Wakili ya rasu bayan yayi shirin tafiya. Nan take dai aka yi maza aka birne Sanatan a Abuja. Shugaban kasa Buhari wanda bai halarci jana’izar ya aika jama’a domin su yi wa mutanen Marigayin ta’aziyya.
KU KARANTA: An kama wasu Makiyayan da ke barna a Garuruwan Najeriya
Abba Kyari ne ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa wajen Mai martaba Sarkin Bauchi Rilwanu Sulaimanu Adam domin ta’aziyyar Sanatan na Bauchi na Kudu wanda shi ne Fagucin Bauchi a lokacin yana raye.
A jiya dai idan ba ku manta ba Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Tawagar sa su ka kai ziyara wajen iyalin Marigayin a gidan sa da ke Gwarimpa. Sanata Wakili ya rasu ne yana da shekarau 58 a Duniya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng