Tsokacin gulma: Mata masu karfi dake tare da gwamnoni
- Karfafan matan dake zagaye da Gwamnoni
- Tasirin mata a dangane da tarihin siyasa a duniya baa bun kokwanto bane haka ma a Najeriya
- Tun a 1986, lokacin da aka kirki Ofishin matar shugaban kasa Maryam Babangida, da kuma gagarumar gudunmuwar data bayar a fagen siyasar Najeriya
- A jihohi da dama na Najeriya, bincike ya nuna mata wadanda suka bada gudunmuwa wajen yanke shawara akan wanda za’a bawa mukamai kuma a inda za’a basu basu mukaman
Gudnmuwar mata a dangane da tarihin siyasa a duniya baa bun kokwanto bane haka ma a Najeriya bai zama daban ba. Tun a 1986, lokacin da aka kirki Ofishin matar shugaban kasa Maryam Babangida, da kuma gagarumar gudunmuwar data bayar a fagen siyasar Najeriya.
A jihohi da dama na Najeriya, bincike ya nuna mata wadanda suka bada gudunmuwa wajen yanke shawara akan wanda za’a bawa mukamai kuma a Ofishinda za’a basu mukaman. A wasu jihohin matan Gwamnoni sun eke rike da komai, duk da cewa basu da wani Ofishi na hakika, amma dai sune suke tsara yanda gwamnatin zata tafi a jihar, kuma wanene za’a bawa wace kwangila.
A rahoton majiyarmu a ranar Lahadi, manema jami’an mu na jihohi, sunyi rubutu akan wadannan karfafan mata da irin tasirin da suke dashi a jihohinsu.
A Kano, matar Gwamna, Hajiya Hafsat, itace ke tafiyar da al’amura ta bayan fage, duk da cewa babu wani Ofishi da aka fada na matar gwamna a jihar, duk da haka, matar gwamnan, Hajiya Hafsat, tanada tasiri sosai a fagen al’amuran yau da kullum na gwamnatin jihar.
Tasirinta akan Gwmnan shine bangaren bada matsayi da bada kwangiloli da sauran harkokin gwamnatin. Ana zargin cewa, matar gwamnan na daya daga cikin dalilan dasuka sa tsohuwar Shugabar Kula da lissafin kudi ta jihar, Hajiya Aisha Muhammed Bello tayi ritaya, a ranar 22, ga watan Fabrairu, 2018.
DUBA WANNAN: Yaje Lahira ya dauko hoto ya dawo yana sayarwa 5000
A jihar Kaduna, lamarin na mata biyu ne, Hajiya Hadiza El-Rufa’i, wadda itace uwar gida, wadda ta karanta Architecture ABU zaria, kuma tayi digiri na biyu a Ingila a fannin rubuce rubuce, wadda take ganin ya kamata a kaddamar da Ofishin matar gwamnan. Tana bawa mijinta shawarwari akan abubuwa kuma tana da tasiri akansa.
Dayar matar Gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Aisha Ummi Garba El-Rufa’I, haifaffiyar Kano ce kuma tana harkar tsara kwalliyar gidaje, ‘yar kauyen Taura ce, a jihar Jigawa, itama tana da tasiri akan gwamnan kamar yanda jami’in mu ya bayyana, ta kuma yi karatu ne ita a Jami’ar Tarayya, 2003, ta karanta Siyarsa kimiyya (Political Science).
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng