Da dumi: Shugaba Buhari ya halarci daurin auren diyar Osinbajo a Abuja, kalli kayatattun hotunan
Shugaba Buhari ya halarci taron daurin waliman daurin auren diyar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; Damilola Osinbajo da Oluseun Bakare a yau Asabar, 17 ga watan Maris, 2018.
Shugaba Buhari ya halarci wannan taro tare uwargidansa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari. Angon dan hamshakiyar maikudi, Mrs Bola Shagaya.

Daga cikin wadanda suka halarci daurin auren sune gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima; gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha; gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura; gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi; da gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Sauran sune gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola; mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, Babagana Munguno; gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da fasto Paul Adefarasin.

KU KARANTA: An yi jana'izzar marigayi Sanata Wakil a Abuja
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng