An yi jana'izzar marigayi Sanata Wakil a Abuja
A yau ne akayi jana'izzar sanata Wakil kamar yadda addinin musulunci ya tanada, an birne marigayi Wakil a makabartar yankin Gudu da ke Abuja misalin karfe 2 na rana bayan anyi masa sallar gawa a babban masallacin babban birnin tarayya Abuja.
An bayar da sanarwan rasuwar Sanatan mai shekaru 58 ne misalin karfe 9 na safiyar yau. Ba'a bayyana takamamen dalilin rasuwar nasa ba amma daya daga cikin hadiman sa ya shaidawa jaridar Premium Times cewa ana tunanin bugun zuciya ne ya yi sanadiyyar rasuwar nasa.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya mika ta'azziyar sa game rasuwar Sanata Wakil
Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa Sanatan yana gudanar da harkokin sa yadda ya saba har ma yana shirin tafiya daurin aure a garin Yola kwatsam sai ya yanke jiki ya fadi ya kuma ce ga garin ku.
Sanatan ya rasu ya bar matan aure guda biyu da yara maza da mata.
kafin rasuwar sa, marigayin ya yi aiki da hukumar yaki da fasakwabri kwastam bayan kammala karatun digiri daga jami'ar Bayero da ke Kano. Ya kai matsayin cpmptrolla a kwastam din kafin ya yi murabus inda ya yi takarar Sanata karkashin jam'iyyar APC kuma ya yi nasara.
Abokan aikin sa da sauran yan Najeriya suna ta mika ta'aziyyar su tare da fadin halayen sa kyawawa.
Kafin rasuwar sa, Wakil ne shugaban Kwamitin rage talauci na majalisar dattawa wanda ke da hakkin bullo da shirye-shirye don rage radadin talauci ga yan Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng