Tsawaita wa'adi: Matasan jam'iyyar APC sun yi fito-na-fito da shugaban jam'iyyar Cif Oyegun
Wasu taron matasa 'ya 'yan jam'iyyar All Progressives Congress, APC mai mulki a karkashin kungiyar su da suka kira ta masu ruwa da tsaki a ranat Alhamis din da ta gabata sun bayyana cewa karin wa'adin mulkin da aka yi wa shugaban jam'iyyar ta APC Cif John Odigie-Oyegun da mukarraban sa bai dace ba.
Matasan dai haka zalika sun bayyana cewa wannan matsayar ta su ne a yayin da suke wani taron manema labarai a garin Abuja jim kadan bayan kammala taron sirri da suka gudanar.
KU KARANTA: Son mulki: Yariman Saudiyya ya daure mahaifiyar sa
Legit.ng ta samu cewa da yake karin haske game da matsayar ta su, kakakin gungun matasan Mista Obekpa ya bayyana cewa matakin da kwamitin zartaswa na jam'iyyar ya dauka kwata-kwata bai dace ba kuma ba da yawun dukkan matasan jam'iyyar ba.
A wani labarin kuma, Shugaban jam'iyyar adawa a jihar Kwara ta Peoples Democratic Party, Cif Iyiola Oyedepo ya sanar da cewa jam'iyyar ta sa ta karbi akalla magoya baya 800 daga jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress cikin 'yan kwanaki kadan da suka wuce.
Shugaban jam'iyyar dai Cif Iyiola shine ya sanar da hakan a yayin da yake zantawa da majiyar mu a garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara a ranar Juma'ar da ta gabata inda kuma ya bayyana cewa wani babban dan siyasa ne Dakta Hanfi Alabere ya jagoranci magoya bayan.
Haka zalika Wata kungiyar matasan jam'iyyar adawa ta kasa watau Concerned Peoples Democratic Party Youths a turance sun fitar da gwamnan jihar Gombe takarar shugabancin kasar nan a zaben shekarar 2019 mai zuwa.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar matasan Malam Sani Bello ya fitar dauke da sa hannun sa a jiya Talata.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng