Soyayya: Yadda wata budurwa ta banka ma kanta wuta akan Saurayi a Jigawa
Wani mummunan lamari ya faru a wani gida dake titin Salihi a unguwar Kofar fada dake cikin karamar hukumar Birnin Kudu na jihar Jigawa, inda wata budurwa ta hallaka kanta saboda Saurayi, inji rahoton Aminiya.
Ita dai budurwa mai suna Hafsat Aminu mai shekaru 19 ta dauki wannan mummunan mataki ne akanta biyo bayan kokarin rabata da saurayinta da aka yi, inda ta daddaki kalanzir, tayi wanka da shi, sa’annan ta bankan ma kanta wuta.
KU KARANTA: Wani matashi dan sara suka ya yi ma kansa yankan rago bayan ya tafka ma dan uwansa mummunar ta’asa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito iyayen Hafsat basa tare da juna, inda tun kimanin shekaru 17 da suka gabata ne mahaifiyar Hafsa da mahaifinta suka rabu, amma tana zama tare da mahaifiyarta da mijinta na yanzu, Malam Abubakar Ahmed Gumel.

A lokacin da Abubakar Gumel da Malama Abu mahafiyar Hafsa suka samu labarin abinda ya faru nan da nan suka garzaya da ita cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya dake Birnin Kudu, da abin yaci tura sai suka garzaya da ita zuwa babban asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, inda ta cika a can.
Da majiyar ta tattauna da saurayinta, Haruna Ibrahim mai sana’ar Tela, ta tabbatar da alakarsa da Hafsa,inda yace kwata kwata basu wuce watanni 8 ba, amma sun shaku matuka, sai dai yace bai ji saboda shi Hafsa ta kashe kanta, yafi tunanin aljanu ne, saboda dama yace tana da aljanu, don koda ta dawo cikin hayyacinta ta ga abinda ya faru, sai da tayi mamaki, a cewarsa.
A nasa bayanin, mahafin Hafsa, Malam Aminu Yakbu, malami a sakandaren Arabiyya ta Birnin Kudu ya tabbatar da mutuwar yar tasa, amma kuma rabonsa da ita sama da shekara 17, tun lokacin da aurensu yam utu da mahaifiyarta.
Malam Aminu yace bana Hafsa ta kammala sakandare, kuma yanzu haka sunanta yana cikin jerin daliban da aka dauka domin yin karatun fannin lafiya a Makarantar Ungozoma ta Birnin Kudu, sai ya ce kwananta ne ya kare kuma ba ya da wani abu da zai fada illa Allah Ya jikanta Ya yi mata rahama.
Sai dai ya musanta batun da ake yadawa na cewa wai za’a mata auren dole ne: “Yaron da ake cewa yana soyayya da ita dan uwana ne ba ya da wata matsala kuma babu batun maganar auren dole, kamar yadda ake bazawa wai za a yi mata shi ne ya sa ta kone kanta. saboda haka batun a ce wai auren dole za a yi mata ta hallaka kanta ba gaskiya ba ne.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng