Dalilin da ya san a hallaka daliban makaranta - Matashi
Wani mutum da ake zargi da tabuwan hankali, Lekan Adebisi, wanda ya hallaka daliban makaranta 2 ya amsa cewa shirye yake fa fuskantan fushin hukuma.
Wannan mumunan abu ya faru ne ranan Litinin a makarantan firamaren St. John’s Anglican Primary School, Agodo, karamar hukumar Ogun Waterside, jihar Ogun.
Matashin ya afka makarantan da da adda ya Sassari dalibai biyu, Mubarak Kalesowo, da Sunday Obituyi, har lahira.
Daga baya hukumar yan sanda jihar suka damke shi ranan Laraba tare da goyon bayan matasan anguwa da mafarauta.
Matashin ya bayyanawa yan jarida cewa ya aikata wannan abu ne saboda kuncin rayuwan da yake ciki.
Ya kara da cewa yunwa ya tuntsura shi saboda makonninshi 2 yanzu bai ci abinci ba kuma babu wanda ya taimaka masa.
KU KARANTA: Ganawar shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin majalisa da daren jiya
“Mako na biyu ban ci abinci ba. Na fita neman kudi amma babu wanda ya taimaka min. Kunci rayuwa ne kaiwa.”
Kwamishanan yan sandan jihar, Ahmed Iliyasu, ya bayyana cewa za’a gurfanar da shi a kotu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng