Wani Alkali ya kara janye hannun sa daga shari’ar Gwamnati da Sambo Dasuki
- Alkalin da shari’ar Kanal Dasuki ke gaban sa a Kotu ya zare hannun sa
- A bara ne dai Alkali Adeniyi Ademola ya mikawa G. Kolawole shari’ar
- Shi ma wannan Alkalin yace ba zai cigaba da shari’ar ba a kai kasuwa
Labari ya zo mana cewa Gwamnatin Tarayya ta yi sanadiyyar da Alkali Gabriel Kolawole da ke shari’ar Sambo Dasuki a Kotun babban Birnin Tarayya ya zare hannun sa daga shari’ar. A bara ma dai wani Alkalin ya zare hannun sa.
Alkali mai shari’a Gabriel Kolawole ya bayyana wannan ne a jiya Alhamis a lokacin da ake kokarin duba wasu hujjoji da Hukumar EFCC ta kawo. EFCC ta kawo wani Sojan kasar mai suna Nicholas Ashinze ne cikin shaidun ta a zaman da aka yi.
KU KARANTA: Kotu ta dakatar da shari'ar Bukola Saraki har sai Baba ta gani
Mai shari’a Gabriel Kolawole ya fusata a yayin da yake kokarin yanke hukunci inda ya zargi Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa da kokarin hana shi gaba ko baya a shari’ar inda yace don haka ya fasa.
Yanzu dai babban Alkalin ya tattara kayan aikin ya mikawa babban Alkalin Kotun Tarayyar na Abuja watau Abdu Kafarithe domin a mika sharia’r zuwa wani Kotun. Alkalin yace ba zai iya cigaba da daukar rainin hankalin EFCC ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng