Wani tsohon Gwamna yace albashin 'Yan Majalisa wasa ne idan ana maganar Gwamnoni
- Albashin Gwamnonin Najeriya ya wuce tunani inji wani tsohon Gwamnan
- A Amurka dai albashin Gwamna ba ya wuce Dala $70,000 zuwa $192, 000
- Kuma albashin Sanata a can Amurka a shekara ba ya wuce Naira Miliyan 50
Wani tsohon Gwamna a Najeriya Peter Obi yace idan mutane su ka ji labarin albashin kowane Gwamna a kasar nan, za su san cewa 'Dan Majalisa ba komai ma yake karba a wata ba.
Peter Obi wanda yayi Gwamna a Jihar Anambra har sau biyu yace abin da ake ba Gwamnonin kasar nan sam bai dace ba. Mista Obi ya bayyana wannan ne a lokacin da ake wajen wani taro na 'Yan jarida masu bin kwakkwafi a Garin Legas.
KU KARANTA: Ku daina tambayar albashin mu - Inji 'Yan Majalisa
Tsohon Gwamnan na Anambra yace idan ya fasa kwan abin da Gwamnoni ke karba a duk wata jama'a za su gane cewa ashe Sanatoci ba komai su ke samu ba da har ake ta wani surutu. Obi yace babu wanda ya san albashin Gwanana.
Obi yake fadawa jama'a cewa da sun san nawa ne albashi Gwamna da ba a same su a wajen taron nan ba. Ya kara da cewa albashin Sanatan a Amurka bai wuce Miliyan 50 a shekara sannan kuma yace Gwamnoni na karbar albashi ne daidai da girman Jihohin su.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng