Yadda aka gudanar da baikon diyar mataimakin shugaban kasa Osinbajo
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dakin taro na Banquet dake fadar shugaban kasa ta Villa ya tumbatsa da manyan baki yayin halartar baiko na babbar diyar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, Oludamilola.
Manyan baki da suka hadar da kwararrun masana, hamshakan 'yan kasuwa, jiga-jigan 'yan siyasa da na hannun daman mataimakin shugaban kasar sun halarci wannan taro na taya murna.
Sai dai jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, an hana bakin shiga wannan dakin taro da wayoyin su na salula, yayin da kuma ba bu ko dan jarida daya na fadar shugaban kasa da aka bari ya kusanci wannan wuri.
Rahotanni sun bayyana cewa, an fara gudanar da wannan taro ne a farfajiyar gidan mataimakin shugaban dake Villa, inda kuma ya dankawa Seun Bakare diyar sa a matsayin wanda zai aure ta a mako mai gabatowa.
KARANTA KUMA: Sabbin kamfanin shinkafa 8 sun kai Najeriya wani mataki na son barka - Bagudu
Legit.ng ta fahimci cewa, an hana 'yan jarida kusantar wannan dakin taro domin kaucewa cecekuce a sakamakon wannan lokaci da ake cikin dimuwa ta hare-haren makiyaya a wasu sassan kasar nan baya ga sace dalibai mata a garin Dapchi na jihar Yobe.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa Ibrahim Magu, ya bayyana cewa fushin doka yana nan tattare da masu handame asusun gwamnati.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng