Ku sadu da Jamilu 'Jamboy' - angon Fatima Dangote kuma matashin mai kudi
Tabbas Hausawa sun yi gaskiya da suka ce wai kwarya ta bi kwarya domin kuwa Naira ce za ta gogi Naira a yayin bikin auren diyar hamshakin mai kudin nan na Afrika Fatima Dangote da kuma angon ta dan tsohon Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya Jamilu Muhammad.
Jamilu dai shine babban da ga mahaifin sa, tsohon shugaban 'yan Sanda Muhammad Dikko Abubakar, wanda yanzu haka an fara shagalin biki sa da amaryar ta sa.
KU KARANTA: Shugaba Buhari zai gana da 'yan majalisu da daren yau
Kamar dai yadda muka samu, za'a daura musu auren ne a sati mai zuwa.
Shi dai Jamilu matashin mai kudi ne kuma yana da sunan gayu da ake kiran sa dashi a cikin abokan sa wato 'Jamboy' wanda kuma hakan ne yake rubuce a jikin lambar motocin sa na alfarma da.
Haka zalika mun samu cewa shi dai Jamilu yana aikin tukin jirgin sama ne, kuma an taba ruwaito cewa tsautsayin hadarin jirgin sama ya taba rutsawa da shi amma Allah ya tsare shi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng