Ku fita daga sabgar mu - 'Yan majalisar wakilai sun gargadi ma su son sanin alawus dinsu
'Yan majalisar wakilai sun yi wasti da bukatar jaridar The Cable na neman su bayyana albashi da alawus dinsu.
Jaridar ta ce mafi yawan 'yan majalisun kan nuna fushinsu a bayyane idan aka tambayesu ko zasu iya bayyana nawa ne albashi da alawus din da su ke karba duk wata.
A kwanannan ne Sanata Shehu Sani, Sanatan Kaduna ta tsakiya, ya fito ya shaidawa jama'a cewar kowanne Sanata a Najeriya na karbar miliyan N13.5 a matsayin kudin gudanarwa bayan albashin N700,000 duk wata.
Mai magana da yawun majalisar wakilai, Abdulrazaq Namdas, ya ki yarda ya bayyana albashi da alawus din da ake biyan 'yan majalisar wakilai.
"Me yasa zan fadi albashi na? Ko kun san nawa ne albashin minista? Ko shi ba jama'a yake wa aiki ba?," inji Namdas, bayan an tambaye shi albashi da alawus dinsa.
DUBA WANNAN: Duk lokacin da na dawo gida sai mijina ya shinshina dan kamfai na - Wata mata ta shaidawa kotu
Da aka shaida masa cewar jama'ar da su ka zabe su ne ke son sanin hakan, sai ya kada baki ya ce: "Sai su yi ta tambaya, babu mai hana su yin tambaya."
Sannan ya kara da cewar jama'a na son sanin albashin dukkan masu rike da mukamin gwamnati amma mai yasa 'yan jarida su ka fi damuwa da na 'yan majalisu kawai.
'Yan majalisar ta wakilai da dama da aka tambaya sun yi guum da bakinsu a kan batun albashi da alawus dinsu tare da bayyana cewar jama'a su kyalesu su sarara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng