Shi Buhari ba abinda ya sani ko da yaushe – Sanata ya soki shugaban kasa

Shi Buhari ba abinda ya sani ko da yaushe – Sanata ya soki shugaban kasa

Sanata mai wakiltar mazabar jihar Abiya, Enyinnaya Abaribe, ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari kan cewa bai da ilimin abubuwan da ke faruwa ko da yaushe.

Sanata Abaribe ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi kan kasha-kashe jihar Kogi da ake zargin makiyaya da yi.

Sanata Atai Aidoko Ali mai wakiltar wani mazaba a jihar Kogi ya kawo kuka majalisa kan kasha-kashen da ke faruwa a jihar.

Yace makiyaya sun kasha mutane 32 a kananan hukumomi 2 a jihar ranan Laraban da ya gabata.

Sanata Abaribe yace subi ga yadda shugaba Buhari ke yi, bai nuna niyyan dakile rashin tsaron da ake fama da shi a kasa ba.

Shi Buhari ba abinda ya sani ko ya yaushe – Sanata ya soki shugaban kasa
Shi Buhari ba abinda ya sani ko ya yaushe – Sanata ya soki shugaban kasa

“Na yarda da shugaban masu rinjaye na majalisa inda yace mu hada kai da bangaren zantarwa. Abinda ban amince da shi ba shine wannan bangaren zantarwan basu amsa cewa su ke da hakkin abubuwan da ke faruwa ba.”

“Muna da shugaban kasa wanda ke cewa bai san sifeto janar na yan sanda ya sabawa umurninsa ba. Shugaban kasan da yace bai san lokacin da hakan ya faru ba. Kowani abu bai sani ba.”

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya isa jihar Neja, ya kaddamar da sabbin gine-gine

Amma shugaban masu rinjaye, Ahmad Lawan, yayi kira ga shugaban majalisa ya hana sanata Abaribe cigaba da sukan shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng