Kungiyar alkalai na kasa (NJC) ta bada umarnin korar alkalai biyu daga bakin aikin su
- Kungiyar NJC ta ba da umarnin korar manyan alkalan Najeriya daga bakin aikin su
- NJC tayi yiwa sauran alkalan Najeriya kashedi akan saba dokokin kungiyar
Hukumar kungiyar alkalai na Najeriya (NJC) ta bada umarnin yiwa wasu alakali guda biyu ritayan dole.
Jastis Thresa Uzokwe, babban alkalin jihar Abia, da kuma Jastis Obisike, na babban kotun tarayya dake jihar Abia, suna cikin akalan da aka yiwa ritayan dole.
An kore su ne bisa laifin saba dokokin kungiyar alkalai na kasa wajen zartar da hukunci.
KU KARANTA : Sarkin Nufawa da Sanata David Umaru sun zargi gwamna Bello da nuna bangarenci da rashin iya shugabanci
Hukumar NJC ta ce ta dakatar da Jastis, Misis Uzokwe’s, da Jastis Obisike,daga bakin aikin su ne bayan an samu sakamakon binciken da akaiyi akan su.
Mai magana da yawun hukumar NJC, Mista Soji Oye, ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, Sannan ya ja kunnen, Jastis S. E Aladetoyinbo, na kotun Abuja da kuma Jastis Olusola Ajibike Williams, na babban kotun tarayya dake jihar Legas akan saba dokokin hukumar NJC.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng