Dokar Hana Kiwo: Gwamnatin Jihar Binuwai za tayi gwanjon dabobin da ta kama

Dokar Hana Kiwo: Gwamnatin Jihar Binuwai za tayi gwanjon dabobin da ta kama

- Gwamnatin jihar Binuwai, ta umurci ma’aikatar kudi, da ta wakilta dillalai da su sayar da dabbobin da aka amsa daga hannun Makiyaya

- Kwamishinan Labaru, Mr Lawrence Onoja, yace an karba dabbobin ne daga hannun Makiyaya a jihar, wadanda suka karya dokar kiwo

- Kwamishinan yace, gwamnati ta bawa masu dabbobin zuwa 19 ga watan Maris, dasu biya tara a Ma’aikatar Gona don karbar dabbobinsu ko kuma ayi gwanjon su

Gwamnatin jihar Binuwai, ta umurci ma’aikatar kudi, da ta wakilta Dillalai da za su sayar da dabbobin da aka amsa daga hannun Makiyaya suna kiwo inda Doka ta hana, a dokar hana kiwo a ko’ina, ta 2017.

Dokar Hana Kiwo: Gwamnatin Jihar Binuwai za tayi gwanjon dabobin da ta kama
Dokar Hana Kiwo: Gwamnatin Jihar Binuwai za tayi gwanjon dabobin da ta kama

Kwamishinan Labarai, Mr Lawrence Onoja, ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai, bayan taron majalissar zartarwa, a ranar Alhamis, a Makodi. Onoja yace, dabbobin an karbesu daga hannun Makiyaya a jihar, wadanda suka karya dokar kiwo. Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta bawa Makiyayan zuwa 19 ga watan Maris, su biya tara a Ma’aikatar Gona don karbar dabbobinsu ko kuma ayi gwanjon su..

KU KARANTA: Kungiyar MURIC tayi tir umarnin dakatar da sauraron korafin hana daliba saka hijabi

Yace, kin yin hakan zai ja a sayar da dabbobin, za’a fara siyar dasu daga 20, ga watan Maris. Onoja, ya kara da cewa Hukumar ta amince da sakin kudi N261m don tallafawa Asusun Noma (IFAD) a jihar.

Ya kuma ce, majalissar ta amince da tsarin kula da kudaden jihar, kamar Kamfanin Gudanarwa (DMO) a tarayya

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164