Talauci na kara yiwa 'yan Najeriya katutu - IMF
- Asusun bayar da Lamuni na Duniya IMF ta fitar da wani rahoto inda ta ce har yanzu tace talauci na kara tsananta a Najeriya
- Asusun ta kuma shawarci shugabannin Najeriya suyi gaggawar bullo da shirye-shirye da zasu inganta rayuwar al'umma
- A rahoton da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa Najeriya kasa ce mai albarkatu da yawa amma rashin shugabani na gari ne ke mayar da kasar baya
Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa talauci na kara yaduwa a tsakanin yan Najeriya duk da cewa kasar ta farfado daga matsin tattalin arzikin da ta fada a baya.
Asusun na IMF ta fitar da wani rahoto inda ta shawarci gwamnatin Najeriya da ta bullo da sabbin hanyoyi da daburun habbaka tattalin arzikin Najeriya inda tace hakan ne kawai zai inganta rayuwar al'ummar Najeriya kuma ta fitar da su daga kangin talauci.
KU KARANTA: Zaben 2019: Ba za mu amince Majalisa tayi amfani da karfin iko wajen canja jadawalin zabe ba - Sanatocin APC
Har ila yau, rahoton da Asusun ya fitar ya kara da cewa babu shakka an samu kankanin cigaban tattalin arziki amma duk da haka akwai sauran rinna a kaba idan akayi la'akari da yadda galibin al'ummar Najeriya ke cigaba da rayuwa cikin fatara.
Asusun ta shawarci Najeriya ta dauki matakin gyara cikin gaggawa ba wai sai lokacin zabe na ya karato ba sannan a fara yiwa al'umma aiki.
Rahoton ya bayyana cewa "Yan Najeriya na rayuwa cikin fatara inda har yanzu sama da 70% na cikin al'ummar suna rayuwa ne a kasa da dallar Amurka daya a kowane rana".
Najeriya dai babban kasa ce a nahiyar Afirka wanda ke da albarkatun man fetur, ma'adinai, yalwar kasar noma da kuma dimbin al'umma sai dai rashin jagoranci sahihi ne ke hana ruwa gudu a kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng