Katinun zabe na dun-dun-dun 62,066 a jihar Katsina na nan a jibge a ofishin INEC
Hukumar zabe ta kasa (INEC) reshen jihar Katsina ta bayyana cewar katinan zabe na dun-dun-dun 62,066 ke jibge ofishin hukumar su na jiran jama'a su zo sun karba.
Kwamishinan hukumar INEC a jihar, Jubril Ibrahim Zarewa, ya ce adadin katinan ya karu ne sakamakon mutuwa, canjin wurin zama ko na aiki da ya samu ma su katinan.
Da yake ganawa da manema labarai a jiya, Zarewa, ya ce, mutane 2,555 ne kacal su ka iya karbar katunan zabensu tun bayan fara sabunta rijistar zabe a watan Afrilun shekarar 2017.
DUBA WANNAN: Motocin jigilar mutane fiye da 10 da dukiyoyi sun salwanta a Legas sakamakon wata gobara
Ya kara da cewar wani bincike ya tabbatar da cewar mafi yawan katinan mallakar dalibai ne wadanda yanzu sun kammala karatunsu sun bar garin.
A shekarar 2019 ne za a gudanar da babban zabe a Najeriya.
Katsina ce jihar da aka haifi shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A wani rahoton Legit.ng na jiya, kunji cewar an kama bindigu a wata mota mallakar wani dan takarar majalisa a jam'iyyar APC, John Aduga. An kama motar ne da wani matashi da ya yi ikirarin shi kani ne wurin dan takarar majalisar a jihar Kogi.
Dakarun soji ne su ka kama motar bayan motar ta lalace a hanya.
Da dakarun sojin ke yi masa tambayoyi, matashin ya ce, ya je dauko mai gyara ne sai kawai ya dawo ya ga jami'an tsaro sun kewaye motar. Ya kara da cewar dan acabar da ya dauko shi ya ba shi shawara ya gudu amma ya ki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng