Jam’iyyar PDP ta bankado wasu gwamnonin APC guda 8 dake yi ma Buhari ‘ingiza mai kan turuwa’

Jam’iyyar PDP ta bankado wasu gwamnonin APC guda 8 dake yi ma Buhari ‘ingiza mai kan turuwa’

Shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus ya bayyana wasu gwamnonin APC guda takwas da yace sune kanwa uwar gami a matakin watsi da dokar sauya jadawalin zabe da shugaba Buhari yayi, inji rahoton Daily Trust.

Secondus ya cigaba da fadin cewa a yanzu haka gwamnonin sun bazama da nufin danne yan majalisar dokokin Najeriya don kada su kwance ma Buhari zani a kasuwa da wannan doka, sai dai bai bayyana sunayensu wadannan gwamnoni ba.

KU KARANTA: Yan matan Dapchi: Shugaba Buhari ya isa garin Damaturu don ganawa da iyayen yan matan

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Secondus ya bayyana haka ne a yayin taron ganawa da shuwagabannin matasan jam’iyyar PDP na jihohi 36, da suka kai ma uwar jam’iyyar ziyara a babban birnin tarayya Abuja.

Jam’iyyar PDP ta bankado wasu gwamnonin APC guda 8 dake yi ma Buhari ‘ingiza mai kan turuwa’
Shuwagabannin APC da PDP

“A talabijin na fara sauraron cewa shugaba Buhari ya yi watsi da kudirin sauya jadawalin zabe, saboda a cewarsa hakan yin karantsaye ne ga hukumar zabe, a ina kuka taba jin haka?, wai wanene INEC, ba INEC na amfani da dokokin da yan majalisa suka krkira bane?

“Ni na rasa, menene abin tsoro a cikin dokar nan? Amma muna tabbatar ma yan Najeriya cewa APC ba ta isa ta murde zaben 2019 ba, yanzu haka APC ta tura gwamnoni guda 8 da nufin su bi yan majalisa don kada su sake duba wannan doka.” Inji Secondus.

Daga karshe Secondus yace ba zasu lamunci abinda APC ke yi ma yan majalisa ba, inda yace ya zama wajibi yan majalisa su yi aikin da yan Najeriya suka zabe su akai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
APC